7 Yuni 2020 - 09:24
​Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Goyi Bayan Shirin Al-sisi Na Zaman Lafiya A Libya

Wasu daga cikin gwamnatocin manyan kasashen duniya sun goyi bayan shirin shugaban kasar Masar Abdulfattah Al-sisi na wanzar da zaman lafiya a kasar Libya.

(ABNA24.com) Wasu daga cikin gwamnatocin manyan kasashen duniya sun goyi bayan shirin shugaban kasar Masar Abdulfattah Al-sisi na wanzar da zaman lafiya a kasar Libya.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawan yankin Tekun Fasha, da suka hada da Saudiyya, UAE gami da Bahrain gami da Joradn, sun goyi bayan shirin Abdulfattah Al-sisi kan dawo da zaman lafiya a kasar Libya.

Haka nan sauran kasashe da suka hada da Amurka da Rasha, sun bayyana shirin na Al-sisi da cewa, zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma kawo karshen yake-yake a kasar ta Libya.

Abdulfattah Al-sisi ya gabatar da shirin nasa ne tare da Halartar Khalifa Haftar, wanda yake yaki da gwamnati Tripoli, inda shirin ya kunshi gudanar da tattaunawa a tsakanin dukkanin bangarorin siyasar kasar ta Libya, tare da kafa gwamnatin hadin akn kasa ta rikon kwarya, wadda za ta kunshi dukkanin bangarori.

A nasa bangaren Khalifa Haftar wanda ya bayyana amincewarsa da wanann shiri, a daya bangaren kuma ya bayyana cewa ba zai amince tattaunawar ta kunshi kungiyoyin ‘yan bindiga ba, wadanda ya ce suna yaki tare da dubban ‘yan ta’adda da suka shigo kasar ta Libya kuma suke yaki a halin yanzu.

Haftar ya ce dole ne Rajab Tayyib Erdogan na Turkiya ya kwashe dubban ‘yan ta’adda da ya shigo da su cikin kasar Libya daga Syria, kafin cimma duk wani daidaito na siyasa a kasar.



/129